<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><lyrics>[V1]
 KORUS
 Albishirin ku mutane
 Salama yau ga duniya
 Gama an haifa mana Mai Ceto
 Emmanuel Allah, tare da mu.

[V2]
 1) Malaiku da suka gani
 Suka rera halleluya
 Sai suka shaida ma makiyaya
 Haifuwar Yesu Ubangiji.
 Korus

[V3]
 2) Makiyaya da suka ji labari
 Suka bar dabbobinsu
 Suka je domin su ga mai ceto
 Yesu makiyayi mai kyau.
 Korus

[V4]
 3) Shehuna da gabas sun gani
 Tauraro Ubangiji
 Suka tafo bisa rakumansu
 Don su gaida sarkin sarauta.
 Korus

[V5]
 4) Tun da kun ji labari
 Na haifuwar Ubangiji
 To sai ku shaida ma mutane
 Haifuwar mai ceton duniya.
 Korus</lyrics>
<title>Albishirin Ku Mutane LW363</title>
<hymn_number>363</hymn_number>
</song>